fbpx
Friday, April 23
Shadow

Siyasa ce ta sa ake tsare Zakzaky da matarsa>>Kasar Amurka

Kasar Amurka ta bayyana cewa siyasa ce tasa ake rike da Shugaban kungiyar IMN wanda aka fi sani da ‘yan Shi’a da matarsa.

 

Amurka ta bayyana hakane a Rahoton data fitar kan kare hakkin bil’adama na shekarar 2020.

 

Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeena na tsare tun bayan kamun da sojoji suka musu a wata Disamba na shekarar 2015. Alkalin kotun tarayya dai ya bada Umarnin sakinsu da basu diyyar Miliyan 25 kowanensu da kuma gina musu gida amma Gwamnati bata aikata hakan ba.

 

A shekarar 2018 gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar dashi a kotu tana zarginsa da cin amanar kasa.

 

“Political prisoners and detainees. IMN’s leader, Sheikh Ibrahim Zakzaky, and his spouse remained in detention. In 2018 the Kaduna State Government charged Zakzaky in state court with multiple felonies stemming from the death of a soldier at Zaria.”

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *