fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Sojoji biyu da ‘yan ta’adda da yawa sun mutu yayin da sojoji ke fafatawa da Boko Haram a jihar Borno

Sojojin Najeriya biyu da ‘yan ta’addan Boko Haram / ISWAP da yawa sun mutu a Borno.

Sojoji sun fafata da ‘yan ta’addan a wani kazamin fada a yankin Bula, Yobe da ke Banki a karamar hukumar Bama.

Wani jami’in leken asiri ya fada wa PRNigeria cewa makiya sun yi yunkurin kai hari kan wata rundunar sojoji.

Jami’an 21 Brigade Bama, a karkashin Operation Hadin Kai, sun yi musayar wuta da abokan adawar na tsawon awanni biyu.

‘Yan ta’addar da ke dajin Sambisa sun afkawa inda suka nufa daga bangarori daban-daban da motoci shida dauke da bindigogi.

“‘ Yan ta’addan sun ja baya a cikin rudani inda da yawansu ke fama da munanan raunuka, suka bar makamai da dama da alburusai da suka hada da bindigar harba jirgin sama da bindigogin AK 47

“Abin takaici, mun rasa jaruman sojoji biyu yayin da muke bin ragowar ‘yan ta’addan da suka tsere bayan artabun,” in ji majiyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *