fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Sojoji sun kashe farar hula 20 wajan kaiwa Boko Haram hare-hare

Fararen hula da dama ne suka mutu sakamakon hare-haren wasu jiragen yaki da aka kai kan mayakan ISWAP a yankin Tafkin Chadi a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce a kalla masunta 20 aka kashe, amma a wasu bayanan sirri da BBC ta gani, rundunar sojin sama ta yi ikirarin cewa masunci daya ne kawai ya rasa ransa sai kuma wasu shida da suka jikkata.

Har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a kan lamarin ba.

Ana ci gaba da samun bayanai daga yankin Kwantan Daban Masara, inda lamarin ya faru a ranar Lahadi da safe.

Ba a san yawan fararen hular da suka mutu ba a harin, sannan babu tabbas kan ko suna da alaka da kungiyar ta ISWAP, wacce ke iko da yankin.

Lamarin na zuwa ne kasa da mako biyu bayan wani harin jirgin yaki da aka kai wani kauye a jihar Yoben Najeriya, wanda ya yi sanadin rasuwar fararen hula da dama, a yankin da sojoji ke yaki da masu ta da kayar baya.

A baya-bayan nan ne ISWAP ta bai wa masunta damar komawa bakin Tafkin Chadi don ci gaba da sana’arsu ta su da sharadin za su dinga biyan kudi.

Hukumomi sun ce an haramta yin su ne a yankin don hana masu ta da kayar bayan samun kudaden shiga.

Kungiyar ISWAP ta balle ne daga ta Boko Haram, wacce dakarun tsaro suka shafe shekara 12 suna yaki da ita.

ISWAP na yawan kai hari kan rundunar sojin Najeriya, kuma a makon da ya gabata ta yi ikirarin kashe sojoji 15 a wani kwanton bauna a jihar Borno da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *