fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 57 a Damboa

Sojoji a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno sun yi nasarar fatattakar yan bokoharam da suka masu kwantan bauna, inda suka kashe ‘yan ta’adda 57 ciki har da kananan yara sojoji.
Mazauna yankin da jami’an tsaro a karamar hukumar sun ce maharan sun zo ne ta hanyar da ta hada Damaboa da karamar hukumar Gwoza da ke jihar.
Gwoza ya kasance halifancin kungiyar Boko Haram da kuma hedikwatarsu har zuwa lokacin da sojoji suka kwato garin a shekarar 2017.
A ranar Alhamis, maharan sun yi yunkurin sake kwace Gwoza, wanda ke da nisan kilomita 156 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno amma sojoji suka yi musu turjiya suka fatattake su.
Sojoji a Damboa sun ce tun da farko an yi musu kwanton-bauna kuma an yi artabu da su. Kodayake, kwanton bauna na biyu da ‘yan ta’addan suka yi ya kasa saboda sojojin sun kasance a shirye sosai kuma sun yi artabu da su, inda suka kashe‘ yan ta’addan 57 tare da kwato makamai da yawa.
Damboa yana kudancin jihar Borno kimanin kilomita 87 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
“Sun yi amfani da daya daga cikin motocinmu da suka sata don kai mana hari.” Wata majiyar tsaro ta fada wa yan jarida “Amma mun yi mu’amala da su, inda muka kashe da dama a yakin.”
“Sojojin sun yi kokari sosai. Sun kasance cikin shirin ko ta kwana tun lokacin da suka kai harin a shekarar da ta gabata a watan Satumba lokacin da ‘yan ta’addan suka farma wani kwamandan sojoji suka kashe shi,” wani mazaunin garin kuma dan kungiyar sa kai na yankin, wanda ya bayyana kansa a matsayin Umar ya shaida wa yan jarida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *