fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a Sambisa

Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 81 a dajin Sambisa.

Sai dai sun rasa soja daya a wani harin nakiya.

Kafar yaɗa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa a yayin tserewa mayaƙan sun lalata gidaje tare da kona wasu.

Sojojin dai sun tarwatsa ƙauyukan ƴan ta’addar damma a yankin garin Bello da Kwoche da Lawanti da Alfa Bula Hassan da Alfa Cross da dai sauransu.

PR Nigeria ta ce wata majiyar leken asiri ta ce sojojin sun gamu da tirjiyar mayaƙan na Boko Haram wadanda suka ajijiye abubuwan fashewa a hanyar da dakarun Najeriyar ke bi.

Kuma a nan ne soja daya ya rasa ransa, hudu suka samu manyan raunuka.

Babban hafsan soji Mejo Janar Ibrahim Attahiru ya yabi sojojin bisa jumurinsu da ƙwazonsu kuma ya buƙaci su ci gaba da jurewa.

A wani ɓangaren kuma, PRNigeria ta ruwaito cewa wasu mayakan Boko Haram da ke tserewa sun afka wa ƙauyukan Zira da Gur a ƙaramar hukumar Biu ta Kudu a jihar ta Borno.

Mayaƙan sun shiga garuruwan ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi a kan babura da motocin yaƙi sannan sun kona gidaje da dama yayin da mazauna ƙauyukan suka tsere.

Jirgin yakin rundunar saman Najeriya sun fatattaki ƴan bindigar daga sama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *