fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Spain Super Cup: Real Madrid ta kai wasan karshe

Kwallon da Toni Kroos ya ci daga kwana ya taimakawa Real Madrid zuwa wasan karshe lashe Super Cup a Spain bayan doke Valencia 3-1 Saudiyya.

Isco da Luka Modric ne suka zira wa Real Madrid sauran kwallayen a ragar Valencia.
Daniel Parejo ya ci wa Valencia kwallo daya a bugun fanariti da na’urar VAR ta bayar.
Valencia ta samu fanaritin bayan Sergio Ramos ya taba kwallon da hannu.
Barcelona za ta fafata da Atletico Madrid ranar Alhamis inda tsakaninsu duk wanda ya yi nasara zai hadu da Real Madrid a wasan karshe ranar Lahadi.
Wannan ne karon farko da aka buga Super Cup tsakanin kungiyoyi hudu, wato biyu da ke saman teburin La liga da kuma wadanda suka buga wasan karshe a Copa del Ray, maimakon yadda aka saba tsakanin kungiyoyi biyu da suka yi nasara a gasannin guda biyu.
Real Madrid ta shiga gasar ne duk da ta kasance matsayi na uku a tebur a kakar da ta gabata saboda Barcelona ta lashe La Liga kuma ta kasance ta biyu a Copa del Ray.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *