fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Ta kacame tsakanin IPOB da Ohanaeze Indigbo: Inda Ohanaeze suka ce basa goyon bayan raba Najeriya, IPOB tace basu isa ba

Cacar baki ta kunno kai tsakanin matasan Inyamurai dake kungiyar IPOB dake son ballewa dan kafa kasar Biafra da kuma dattawan yankin dake cikin kungiyar Ohanaeze Indigbo.

 

Shugaban Ohanaeze Indigbo, Dr. George Obiozor ya bayyana cewa, basa goyon bayan ballewa daga Najeriya a kafa kasar Biafra.

 

Ya bayyana hakane ga manema labarai a Enugu, yace amma kuma ba zasu amince da cutarwar Gwamnati akan kabilar Inyamurai ba.

 

Ya bayyana cewa, amma yana kura ga matasan Inyamurai cewa babu nasara a tare da tayar da hankali da kisa da kona kayan Gwamnati. Yace komai daren dadewa wannan abu da ake zai zo ya wuce.

 

Saidai kungiyar IPOB ta bakin kakakinta Emma Powerful ta bayyana cewa, basu neman goyon bayan Ohanaeze Indigbo wajan kafa kasar Biafra.

 

Yace kuma babu abinda zai hanasu kafa kasar.

However, spokesperson of the proscribed Indigenous People of Biafra, Emma Powerful, dismissed Obiozor’s remark, insisting that nothing can stop the actualisation of Biafra.

He said: “They can say whatever they like. The general public has taken Biafra freedom. The youths are not begging them to support us because their hallucinations cannot stop us. We are going home and they will follow us soon.

“They can’t talk because they are afraid of their masters in the North and Aso Rock.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *