fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Ta kacame tsakanin ‘yan IPOB sun fara kashe junansu

‘Yan IPOB sun fara bin junansu da kisa ga dukkan alamu inda aka fara samun baraka a a tsakaninsu.

 

A baya an kashewa kungiyar babban Kwamandanta me suna Ikonso wanda dagashi dai Nnamdi Kanu.

 

Lamarin ya tayarwa kungiyar hankali sosai inda Inyamurai da yawa suka nuna rashin jin dadinsu. Tun a wancan lokaci ne kungiyar ta fara zargin cewa wasu na cikin gidane suka ci amanar Ikonso.

 

Kungiyar ta gano wani wanda take zargin shine ya labartawa jami’an tsaro inda Ikonso yake har aka je aka kasheshi. IPOB ta kashe mutumin a wani waje da yake boye tsakanin Jihar Imo da Anambra,  kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.

 

Saidai ba’a bayyana sunan mutumin ba. Wasu na cewa mutumin dan IPOB ne inda wasu ke cewa dan leken Asiri ne kawai.

“Ikonso Don was a well-known hardcore IPOB member. When the ESN was launched, he joined and participated in several operations, rising to later become a commander. He was going to his village in Umuoma alongside other ESN members when they were ambushed.

 

“He was targeted and killed after some of the Igbo he was fighting for gave out his details to the security forces,” a source had explained.

 

“His photographs were also shared on social media by a friend and he was given away as the ESN commander. That was the same place his photograph with Nnamdi Kanu was obtained,” another source said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *