fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Tag: Ngozi Okonjo Iwaela

Amurka ta Amince Ngozi Okonjo Iwaela ta Jagoranci WTO

Amurka ta Amince Ngozi Okonjo Iwaela ta Jagoranci WTO

Uncategorized
Gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta kawo ƙarshen takaddamar da ta hana naɗa mace ta farko da za ta jagoranci Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) bayan da ta bayyana goyon bayanta ga tsohuwar ministar kuɗin Najeriya. Ngozi Okonjo-Iweala ce ke kan gaba wajen zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar cinikayyar ta duniya kafin gwamnatin Mista Trump ta ce tana goyon bayan wata matar ta daban, Yoo Myung-hee ta Koriya ta Kudu. A halin da ake ciki, Ms Yoo ta janye daga takarar shugabancin ƙungiyar. Idan aka tabbatar ma ta muƙamain, Dr Okonjo-Iweala za ta kasance mace ta farko, kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar. A watan Oktobar bara kwamitin zabe na ƙungiyar ta WTO ya bayyana sunan Okonjo-Iweala ga mambobin ƙungiyar 164, yana cewa ta dace...
PDP ta jinjinawa shugaba Buhari kan goyon bayan Ngozi Okonjo Iwaela

PDP ta jinjinawa shugaba Buhari kan goyon bayan Ngozi Okonjo Iwaela

Siyasa
Jam'iyyar PDP ta jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan goyon bayan da ya baiwa tsohuwar minitar Kudi, Ngozi Okonjo Iwaela har ta zama daraktar cibiyar kasuwanci ta Duniya, WTO.   Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar kamar yanda, kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito. Yace kasancewar Ngozi a matsayin daraktar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya mace ta farko sannan kuma 'yar Africa ta farko abin Alfahari ne sannan kuma suna jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya ajiye siyasa ya goyi bayanta.   Yace suna kuma jinjinawa shugaban kasar da ya nuna goyon baya ga shugaban bankin raya Africa, Akinwunmi Adesina.   “Okonjo-Iweala’s victory is a reward for hard work and commitment to excellenc...
Da Duminsa:Ngozi Okonjo Iwaela ta Zama Daraktar cibiyar kasuwanci ta Duniya, WTO

Da Duminsa:Ngozi Okonjo Iwaela ta Zama Daraktar cibiyar kasuwanci ta Duniya, WTO

Siyasa
'Yar Najeriya, tsohuwar Ministar Kudi, Ngozi Okonjo Iwaela ta zama Daraktar cibiyar kasuwanci ta Duniya, WTO. Ngozie ta lashe wanan mukami ne bayan data kayar da abokiyar takararta 'yar kasar Koriya ta Kudu, Yoo Myung hee da tazarar kuri'a mai yawa.   Ta samu goyon Bayan Kasashen Africa da ma wasu kasashe da dama. A baya ta rike daraktar bankin Duniya, sannan kuka ta yi aiki da Twitter da Global Vaccine Alliance.   Kasar Amurka ta goyi bayan Yoo, yayin da kasashen turai kuma suka goyi bayan Ngozi.   Mrs. Okonjo-Iweala received widespread support from Africa and other continents for her role. She was a former World Bank executive who has sat on the boards of several international organisations, including Twitter and the Global Vaccine Alliance. Her...
Zamu ci gaba da baki goyon baya har ki yi nazarar zama shugabar WTO>>Shugaba Buhari ga Ngozi

Zamu ci gaba da baki goyon baya har ki yi nazarar zama shugabar WTO>>Shugaba Buhari ga Ngozi

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo Iwaela tabbacin zai ci gaba da bata goyon bayan ganin ta zama shugabar cibiyar Kasuwanci ta Duniya.   An dai ta gurzawa da Ngozi har ta zama yanzu su biyu ne suka rage wanda za'a dauki daya daka cikinsu ta zama shugabar WTO. Shugaban kasar ya baiwa Ngozi wannan tabbaci ne a yayin ziyarar da ta kai masa jiya a fadarshi dake Abuja.   Hadimin shugaba Buhari,  Bashir Ahmad yace shugaban ya bayyana cewa zasu yi dukkan mai yiyuwa wajan ganin cewa Ngozi ta samu wannan mukami, ba wai dan kawai ta na 'yar Najeeiya ba sai dan ta cancanta. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1315685660519469058?s=19 “I assure you that we will do all that we can to ensure that you emerge as the Director...
Tsohuwar Ministar PDP ta bada Hakuri kan cewa wannan Hoton yanda ake rabawa ‘Yan kasar Rwanda tallafin abincine bayan gano cewa hoton daga kasar Gambia ya fito

Tsohuwar Ministar PDP ta bada Hakuri kan cewa wannan Hoton yanda ake rabawa ‘Yan kasar Rwanda tallafin abincine bayan gano cewa hoton daga kasar Gambia ya fito

Siyasa
Tsohuwar ministar Kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iwaela da a jiya ta saka wani Hoton kayan rabon Abinci wanda tace daga kasar Rwanda ne kuma lamarin ya jawo cece kuce sosai a yanzu ta cire hoton kuma ta bayar da hakuri.   Ngozi ta bayar da hakurinne a shafinta na Twitter inda tace wani ne ya aika mata da hoton, tace amma dai abinda take son yin nuni dashi shine a kyautatawa 'yan Najeriya. https://twitter.com/NOIweala/status/1247953910146519042?s=19 Dama dai hadimi  shugaban kasa,Bashir Ahmad ya bayyana cewa hoton da Ngozin ta yi amfani dashi ba daga kasar Rwanda yake ba daga Gambia yake. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1247951955302977538?s=19 Gwamnatin tarayya dai na Rabawa mutane mafiya bukata kudin tallafi na Naira Dubu 20.
“Adawo da Okonjo Iweala Najeriya Domin ta Tallafawa Najariya daga Mashash-sharar Tattalin Arzikin Kasa”

“Adawo da Okonjo Iweala Najeriya Domin ta Tallafawa Najariya daga Mashash-sharar Tattalin Arzikin Kasa”

Siyasa
A maido da Dr. Okonjo-Iweala don ceto tattalin arzikin Najeriya daga Mashash-shara, Gbagi ya fada wa Gwamnatin Tarayya.   Tsohon Ministan Ilimi, Olorogun Kenneth Gbagi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki kwararan matakai don dawo da Dokta Ngozi Okonjo-Iweala don yi wa kasa aiki.   Gbagi ya ce Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayinta na kwararriyar masaniya kan tattalin arziki, tabbas tana iya taimakawa Najeriya wajen fitar da kasar daga fadawa cikin rudani.   Gbagi, wanda ke mayar da martani ga nadin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar Ministar Kudi, a matsayin zabin da a kai mata na zama memba a matsayin mai bada shawara kan tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu.   Gbagi ya bayyana shi a matsayin babban abin alfahari da nasara, ya kuma kara jadd...