fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Tag: Sanata Shehu Sani

A lokacin baya da muka rika jawo hankalin gwamnati kan matsalar tsaro an ce mu makiyan Buhari ne>>Sanata Shehu Sani

A lokacin baya da muka rika jawo hankalin gwamnati kan matsalar tsaro an ce mu makiyan Buhari ne>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu sani, tsohon sanata dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana cewa an rika musu fassarar cewa su makiyan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ko kuma suna so su bata sunansa a idon 'yan Najeriya yayin da suka rika bayyana magsalar tsaro.   Yace a lokacin suna majalisa, sun rika kokarin jawo hankalin shugaban kasar kan magsalar tsaro a Kaduna, Zamfara da Katsina tun bata kai haka ba.   Yace amma na kusa da shugaban kasar sun rika gaya masa cewa su makiyansa ne ko kuma suna son bata masa sunane.   Yace idan ba'a dauki mataki ba akwai matsala nan gaba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Sunnews inda yace kuma baya nadamar duk abinda yayi lokacin yana sanata.   A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Gw...
Kaduna yanzu ta zama cibiyar ‘yan bindiga>>Shehu Sani

Kaduna yanzu ta zama cibiyar ‘yan bindiga>>Shehu Sani

Siyasa
Shehu Sani, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, a ranar Asabar ya koka kan yadda 'yan fashi suka mayar da jihar Kaduna cibiyar su. Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga sace wasu mambobin cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, a jihar. An ce 'yan bindiga sun sace mambobin RCCG na lardin Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kafachan da yammacin ranar Juma'a. An kama motar ta RCCG a hanyar Kachia - Kafachan kuma masu satar mutane sun tafi da dukkan fasinjojin. A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka sace wasu mutane 8 a jihar Kaduna. Fasto Olaitan Olubiyi, Shugaban yada labarai da hulda da jama'a na RCCG, ya tabbatar da satar mutanen. Bai fitar da cikakken bayani ba a kan ainihi da yawan wadanda abin ya shafa. Da ya...
Ku maida hankali don sakin daliban Kaduna>>Shehu Sani ga Gwamnatin Tarayya

Ku maida hankali don sakin daliban Kaduna>>Shehu Sani ga Gwamnatin Tarayya

Tsaro
Shehu Sani, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya yi kira da a saki daliban jihar Kaduna da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka sace. Dalibin kwalejin gandun dajin Kaduna da 'yan ta'adda suka sace makonni da suka gabata har yanzu ba a sake su ba. A ranar Litinin ne iyayen daliban suka yi zanga-zanga a Kaduna, suna kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su yi aiki tare don tabbatar da an sako yaransu cikin gaggawa. Da yake kara muryarsa ga kiran nasu, Shehu Sani a shafinsa na Twitter ya bukaci gwamnatin shugaba Buhari da ta tsananta kokarin ganin an sako daliban. Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya sun yi zanga-zanga. “Dole ne Gwamnati ta kara himma don ganin an sake su. Ba mu da l...
Shin wai ya aka yi Rarara bai lashe kyautar gwarzon waka ta Duniya ba,Grammy Award?>>Sanata Shehu Sani

Shin wai ya aka yi Rarara bai lashe kyautar gwarzon waka ta Duniya ba,Grammy Award?>>Sanata Shehu Sani

Nishaɗi
Sanata Shehu Sai ya tambayi shin ko me yasa Mawakin Suyasa, Dauda Kahutu Rarara bai lashe kyautar Gwarzon mawakin Duniya ta Grammy award ba?   A daren jiya ne dai wasu mawakan Najeriya 3, Burna boy,  Wizkid da Tiwa Savage suka lashe kyautar.   Sanata Shehu Sani bayan ya tayasu murna, ya bayyana cewa har yanzu ba'a gayyaci Rarara zuwa bada kyautar Grammy ba.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1371213061701443585?s=19
Mawakan Najeriya,  Burna boy, Wizkid da Tiwa Savage sun lashe kyautar waka ta Duniya, Grammy award

Mawakan Najeriya, Burna boy, Wizkid da Tiwa Savage sun lashe kyautar waka ta Duniya, Grammy award

Nishaɗi
Mawakin Najeriya,  Burna Boy ya lashe kyautar Waka ta Duniya, Grammy award.   Ya lashe kyautar ne da kundin wakarsa na Twice as Tall.   A martaninsa, Burna boy ya bayyana cewa dama yasan watarana zai yi nasara saboda duk abu me kyau na bukatar a masa tsari. https://twitter.com/burnaboy/status/1371216780828553224?s=19   Ya saka hotonsa tare da mahaifiyarsa inda suke murnar wannan nasara da ya samu tare.   https://twitter.com/burnaboy/status/1371221777859371018?s=19   Shima Mawakin Najeriya, Wizkid ya lashe kyautar ta Grammy a wakar da suka yi da Beyonce ta Brown Skin Girl.   Itama Mawakiya Tiwasavage ta yi nasarar lashe Kyautar ta Grammy a wakar da suka yi da Coldplay.   Sanata Shehu Sai ya tayasu Murna. &nbs...
Bai kamata maganar saka Hijabi a makarantu ba ya jawo tashin hankali>>Sanata Shehu

Bai kamata maganar saka Hijabi a makarantu ba ya jawo tashin hankali>>Sanata Shehu

Siyasa, Uncategorized
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, Bai kamata maganar saka Hijabi a makarantu ba ja jawo tashin hankali.   Yace kamata yayi wanda ke son 'ya'yansa su saka Hijabi su saka, wanda kuma bai so kada a tilasta masa. Yace makarantun jihar Kaduna sun dade suna amfani da Hijabi a matsayin kayan zuwa Makaranta.   Jihar Kwara dai ta sake rufe makarantu 10 saboda Rashin Fahimta kan saka Hijabin Dalibai zuwa Makaranta.   The Hijab as a School Uniform should NOT cause any controversy.Those who want their Children to wear it,should be allowed to wear it.Those who don’t want their Children to wear it,should NOT be forced to do so.Dual uniforms has been used in Kaduna for over two decades.
Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa tubabbun Boko Haram ke sake komawa kungiyar

Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa tubabbun Boko Haram ke sake komawa kungiyar

Siyasa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa Tubabbun Boko Haram na yiwa kungiyar leken Asiri a cikin jama'a sannan kuma su sake komawa cikinta.   Gwamnan ya nemi a rika yankewa 'yan Boko Haram din hukunci kawai idan an kamasu.   A martaninsa ga wannan lamari, Tsohon sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, yana baiwa mutane dalilin da yasa 'yan Boko Haram da suka tuba ke sake komawa kungiyar shine Jini ya fi ruwa Kauri.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1367772434166865920?s=19    
Hadimin Gwamnan Kano da Ganduje ya kora ya roki Sanata Shehu Sani ya bashi aiki

Hadimin Gwamnan Kano da Ganduje ya kora ya roki Sanata Shehu Sani ya bashi aiki

Siyasa
Salihu Tanko Yalasai, Tsohon Hadimin Gwamnan Kano da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kora daga aiki saboda sukar gwamnatin shugaba Buhari kan matsalar tsaro ya roki sanata Shehu Sani ya bashi aikin yi.   Salihu wanda DSS suka kama amma daga baya aka sakeshi saboda kira da yayi ga shugaba Buhari yayi Murabus kan matsalar tsaro ya bayyana cewa, Sanata Shehu Sani ya bashi aiki dan su tattauna kan zama a gidan yari.   Saidai Sanata Shehu Sani yace masa ya kwantar Da hankalinsa yana mataki na farko ne.   Salihu yace ashe dai akwai sauran aiki a gabansa.   https://twitter.com/dawisu/status/1367372085203460096?s=19
Tsaffin shuwagabannin tsaro sun yi sa’a ba lokacin mu bane>>Sanata Shehu Sani

Tsaffin shuwagabannin tsaro sun yi sa’a ba lokacin mu bane>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
A jiyane dai Majalisar Dattawa ta tantance tsaffin Shuwagabannin tsaro, Janar Tukur Yusuf Buratai,  AVM Sadiq Abubakar, Janar Abayomi Olonisakin, Ibok Ekwe Ibas a matsayin jakadun Najeriya.   Wannan Tantancewa ta jawo cece-kuce sosai inda jama'a da dama suka rika bayyana ra'ayoyinsu akai.   Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa tsaffin shuwagabannin tsaron sun yi sa'a basu ne suka tantancesu ba.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1364216475469381632?s=19
Rashin tausayin Al’umma ne , da kace ko a Amurka ana satar yara>>Martanin Shehu Sani ga Lai Mohammed

Rashin tausayin Al’umma ne , da kace ko a Amurka ana satar yara>>Martanin Shehu Sani ga Lai Mohammed

Tsaro
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yace, rashin nuna tausayi ne ga iyayen daliban Kagarada aka sace, idan kace ko a Amurka ana satar yara. Shehu Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta na Twitter, ya ce wannan maganar bata dace ba sam. Hakane ya biyo bayan maganar da Minista yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya yi, Inda yace satar yara a makarantu abu ne wanda har kasashen da suka ci gaba suna fama da, kuma har misali ya ba suwa da kasar Amurka.