fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Tag: Shehu Sani

Ka dainawa ‘yan Bindiga gargadi da Turanci, ka rika musu da yaren da zasu gane>>Sanata Shehu Sani ga Shugaba Buhari

Ka dainawa ‘yan Bindiga gargadi da Turanci, ka rika musu da yaren da zasu gane>>Sanata Shehu Sani ga Shugaba Buhari

Tsaro
Sanata Shehu Sani ya baiwa shugaba kasa, Muhammadu Buhari shawarar cewa ya daina wa 'yan Bindiga gargadi da Turanci, ya rika musu da yaren da zasu gane.   Sani na martanine akan gargadi kala-kala da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yawa 'yan Bindiga amma ga dukkan alamu basu ji ba, sai ma kara kaimi suke wajan kai hare-hare.   Sanata Sani ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, tunda dai umarnin da shugaba Buhari yaki amfani ta yaren turanci, ya kamata ya rika gayawa 'yan Bindigar da yaren da zasu gane. “All warnings issued to the bandits should be made in the local language they can understand. Warning them in English is so far futile.”
Ku wadata yan Najeriya da kayan kare kai>>Shehu Sani ga ministan tsaro

Ku wadata yan Najeriya da kayan kare kai>>Shehu Sani ga ministan tsaro

Tsaro
Shehu Sani, tsohon dan majalisar jihar Kaduna ya maida martani ga maganar da Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya yi, inda ya shawarci 'yan Najeriya da su kare kansu daga' yan fashi. Janar din mai ritaya yayin da yake magana a kan rashin tsaro da hare-haren ’yan fashi a wasu sassan Najeriya, ya shawarci’ yan Najeriya da kada su zama matsorata inda ya kara da cewa a wasu lokuta ‘yan bindigar na samun harsasai kadan ne kawai. Ya gaya wa ‘yan kasar su kasance a farke a kowane lokaci su kare kansu. Dangane da kalaman Ministan, Sani ya fada wa Magashi da ya wadata ‘yan Najeriya da kayan aiki domin kar su zama matsorata yayin da‘ yan fashi ke kai hari. A shafinsa na Twitter, tsohon dan majalisar dokokin na Kaduna ya rubuta: “Idan Ministan Tsaro yana ba da umarnin kare kai, ya ka...
Abinda za’a yi nan gaba shine kiran taron sirri da kuma yin gargadi>>Sanata Shehu Sani

Abinda za’a yi nan gaba shine kiran taron sirri da kuma yin gargadi>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
Sanata Shehu Sani da yake magana me kama da habaici akan matsalar tsaron data kunno kai, yacs abinda za'a yi nan gaba shine kiran taron gaggawa.   Yace a karshe kuma a bata umarni na karta kwata ko kuma gargadi.   Next will be closed door meeting followed by marching orders or strong warning.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1333058036932481025?s=19
Yanda Jihohi ke ikirarin makudan kudaden da suka yi asara dalilin wawaso watakila sai an sayar da har rufin ginin CBN kamin a biyasu diyya>>Sanata Shehu Sani

Yanda Jihohi ke ikirarin makudan kudaden da suka yi asara dalilin wawaso watakila sai an sayar da har rufin ginin CBN kamin a biyasu diyya>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu Sani yayi magana kan ywan kudaden da jihohi ke cewa sun tafka asararsu dalilin zanga-zangar SARS da wawason kayan Abinci dana amfani da ya biyo baya.   Sanata Sani yace jihar Legas tace ta tafka Asarar tiriyan 1 sannan ita kuma Filato ta tafka asarar Biliyan 75. Yace idan sauran jihohin suka bayyana asarar da suka yi sai an sayar da Har rufin saman CBN kamin a mayar musu da asarar.   Lagos said they lost one Trillion and Plateau said they lost 75Billion;by the time other states posted their figures even the roof and Toilets fittings of the CBN building would be shared for compensation. https://twitter.com/ShehuSani/status/1322243219481120768?s=19
Da Obasanjo yayi gargadi sai suka caccake shi amma da Osinbajo yayi sai suka yi shiru>>Shehu Sani

Da Obasanjo yayi gargadi sai suka caccake shi amma da Osinbajo yayi sai suka yi shiru>>Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu Sani yayi magana akan gargadin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi na cewa Najeriya ka iya rabewa idan ba'a yi wani abin a zo a gani ba kan matsalar dake damunta.   Kalaman dai sun jawo cece-kuce inda wasu suka goyi bayansa, wasu kuwa caccakarsa suka yi.   A martaninsa, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, da Obasanjo da yayi gargadi saiaka masa caa, ana caccakarsa, amma Osinbajo da yayi irin wannan gargadi, sai aka yi shiru. https://twitter.com/ShehuSani/status/1310865410749853696?s=19   Kungiyar dattawa Arewa ta ACF ta ja kunnen Osinbajo da cewa yayi hankali da kalaman da yake furtawa a matsayinsa na shugaba.
Titin Baga ya zama Tarkon Mutuwa ya kamata a kaurace masa har sai an samu isashshen tsaro>>Sanata Shehu Sani

Titin Baga ya zama Tarkon Mutuwa ya kamata a kaurace masa har sai an samu isashshen tsaro>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
Sanata Shehu Sani ya kara bayyana alhininsa kan kisan da Boko Haram ta wa wasu mutane kimanin 30 a hanyar Baga dake jihar Borno.   Boko Haram ta kaiwa tawagar gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum hari saidai shi gwamnan ya tsallake, inda wasu Rahotanni kuma suka nuna cewa, baya cikin tawagar dan shi ta jirgin sama ya shiga Baga. Sanata Sani a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa hanyar Baga ta zama tarkon Mutuwa wadda ya kamata a kaurace mata har sai tsaro ya samu. https://twitter.com/ShehuSani/status/1310143434968227840?s=19 Sanata sani ya kuma yi kira da a dauki nauyin karatun 'ya'yan mamatan da kula da rayuwarsu inda ya mika sakon ta'aziyyar sa.
Sanata Shehu Sani, Gali Umar Na Abba, Femi Falana da wasu sauran manyan ‘yan Najeriya na shirin bude sabuwar jam’iyya

Sanata Shehu Sani, Gali Umar Na Abba, Femi Falana da wasu sauran manyan ‘yan Najeriya na shirin bude sabuwar jam’iyya

Uncategorized
Wasu fitattun 'yan Najeriya sun hada kai inda suka yi shirin fito da wata sabuwar jam'iyya da a cewarsu zata fitar da kasarnan daga matsalar da take ciki.   A yanzu dai sun sakawa kungiyar tasu sunan National Consultative Front kuma sun bayyana cewa bayan tattaunawa da kuma tuntuba da masu ruwa da tsaki, sun yanke shawarar buxe sabuwar jam'iyyar.   Daga cikin membobin wannan kungiya 30 akwai Femi Fala(SAN), Sanata Shehu Sani, Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba, Alhaji Shattima Yarima,  Obigeli Ezekwesili dadai sauransu.   Sun kara da cewa sun damu da matsalar hare-haren ta'addanci dake faruwa a kasarnan da da suka hada da sace mutane dan neman kudin fansa.
Masu kona hotunan ‘yan Adawa shekara daya data gabata yanzu suna kona hotunan gwanayensu>>Sanata Shehu Sani

Masu kona hotunan ‘yan Adawa shekara daya data gabata yanzu suna kona hotunan gwanayensu>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
A makon daya gabatane muka ga yanda wasu matasa daga 'yan Tumaki, johar Kastina da suka fito zanga-zanga suka kona fastar shugaban kasa, Muhammadu Buhari data gwamna Aminu Bello Masari.   Lamarin ya dauki hankula sosai inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Sanata Shehu Sani shima yayi magana kan wanna batu duk da cewa be ambaci suna ba.   Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, Wanda suke lalata fastocin 'yan adawa shekara guda data gabata, a yanzu sune ke lalata fastocin gwanayensu. https://twitter.com/ShehuSani/status/1270646705801826304?s=19 Sanata Shehu Sani dai kan bayyana ra'ayoyishi akan al'amuran dake faruwa a Najeriya daga Lokaci zuwa Lokaci.
Abin takaici ne yanda wasu samari suke lissafa kudin da suke kashewa budurwa kuma war su nemi a biyasu>>Sanata Shehu Sani

Abin takaici ne yanda wasu samari suke lissafa kudin da suke kashewa budurwa kuma war su nemi a biyasu>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu Sani tsohon dan majalisar dattijai me wakiltar Mazabar Kaduna ta tsakiya yayi martani kan ikirarin saurayin matar da shugaban hukumar shige da fici na kasa, Kwastam watau Hamid Ali yayo na cewa a biyashi kudin da ya kashemata   Sanata Shehu Sani duk be ambaci suna ba amma da yawa sun yi ittifakin cewa yana maganane akan batun na maganar biyan kudi. A dazune dai hutudole ya kawo muku yanda saurayin matar da Hamid Ali ya aura ya fito yake neman a biyashi kudin da ha kashe mata inda yayi ikirarin kaita kasashe da dama.   Shehu Sani a shafinshi na Twitter kamar yanda hutudole ya samo ya rubuta cewa abin takaicine yanda yanzu maza idan suna soyayya da mace sai su rika lissafa kudin da suka kashe mata kuma har su nemi a biyasu. https://twitter.com/She...
A wallafa sunayen mutanen da aka baiwa dubu 20>>Shehu Sani

A wallafa sunayen mutanen da aka baiwa dubu 20>>Shehu Sani

Siyasa
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya,Sanata Shehu Sani ya hankalin cewa a wallafa sunayen mutanen da aka baiwa Dubu 20.   Yayi wannan maganane a shafinshi na sada zumunta inda duk da cewa bai bayyana ba amma alamu sun nuna da gwamnatin tarayya yake. https://twitter.com/ShehuSani/status/1246386912748847105?s=19 Gwamnatin tarayya karkashin ma'aikatar kula da ibtila'i da tallafawa jama'a tace ta fara rabon Dubu 20 ga mutane mafiya bukata a fadin Najeriya