fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Tallafin wutar lantarki na cin biliyan N30 a kowane wata, – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce yawan kudin da ake kashewa kan tallafin wutar lantarki kowane wata a Najeriya ya kusan biliyan N30.

Ya bayyana cewa tallafin da gwamnati ke bayarwa a kan wutar lantarki ta ragu da biliyan N20 kowane wata biyo bayan ci gaba da aka samu na karbar harajin wutar lantarki daga kamfanonin rarrabawa.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata takaddara kan ci gaba da kuma dubawa game da bangaren wutar lantarkin Najeriya. An samu wannan takarda ne daga ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da ke Abuja.

A watan Fabrairun bana, Ministan Makamashi, Sale Mamman, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafi ga samar da wutar lantarki a duk fadin kasar har zuwa sama da biliyan N50 duk wata.

Mamman ya bayyana cewa kudin tallafin ya kasance ne saboda gwamnati ta damu da yawan korafin da ‘yan Najeriya ke yi game da karin kudin wutar lantarki da ba za a iya kaucewa daga lokaci zuwa lokaci ba.

Ya ce an samar da kudaden ne domin kara gibin da kamfanonin rarraba wutar suka yi wadanda suka gaza rage kudin da aka kashe na dimbin wutar lantarkin da kamfanonin samar da wutar suka samar musu.

Ya ci gaba da bayanin cewa biyo bayan karamin kudin da aka samu a tsarin harajin, tallafin ya ragu amma duk da haka ya na da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *