fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Tattalin Arzikin Najeriya Ka Iya Habbaka Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya>>Masana

Rikici a gabas ta tsakiya ka iya haddasa tashin farashin danyen mai a duniya, lamarin da masana ke ganin hakan zai iya shafa ko habbaka tattalin arzikin Najeriya.
A dai dai lokacin da kasar Iran ta sha alwashin daukar fansar harin da Amurka ta kai ta sama, da ya hallaka babban kwamandan zaratan sojojin juyin juya hali na Iran, Qassem Soleimani, manazarta na ganin zai iya shafar dukkan yankin gabas ta tsakiya, da ma wasu kasashen duniya.

Farfesa Bello Muhammad Bada, malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, kuma mai sharhi akan al’amura, ya bayyana yadda lamarin zai shafi kasashen Africa musamman Najeriya mai arzikin man fetur, a bangaren tattalin arziki.
A cewar Farfesa Bello, Najeriya ta dade ba ta samu kudin shiga ba kamar wanda ta samu lokacin yakin Iraqi, saboda haka ake ganin idan wani tashin hankali ya faru tabbas farashin mai zai tashi, inda kasashen da ke fitar da Mai irin su Najeriya zasu kara samun kudin shiga.
Sai dai a bangare guda kuma, bayan karin kudin shigar da Najeriya za ta samu, za ta sayo tataccen mai wanda sai ta biya sama da abin da take biya a baya.
VOAhausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *