fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Tauraron dan wasan Real Madrid Luka Jovic ya kamu da cutar Covid-19

Kungiyar Real Madrid ta samu munanan labarai gami da hutun wasanni kasashe da yan wasanta suka tafi, yayin da yanzu kaftin din tawagar Segio Ramos zai rasa wasanni uku saboda raunin daya samu kuma Luka Jovic ya kamu da cutar korona.

Real Madrid ta tabbatar da cewa dan wasan nata ya kamu da cutar ne bayan daya dawo daga bugawa kasar sa ta Serbia wasanni. A ranar laraba kasar Serbia ta tabbatar da cewa ma’aikatan ta guda hudu tare da yan wasa uku sun kamu da cutar korona kuma shi Jovic bai kamu ba a wancan lokacin.
Amma yanzu bayan dawowar shi daga kasar ya kamu da cutar kuma zai cigaba da killace kanshi har sai ya warke. Luka Jovic ya zamo dan wasan Real Madrid na biyar daya kamu da cutar bayan Mariano,Militao,Casemiro da Eden Hazard sun kamu da cutar wanda yanzu gabadayan su sun warke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *