fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Tinubu ya ziyarci Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin jagoran jam’iyyarsu ta APC, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.

Da isarsa ne kuma suka wata ganawa cikin sirri.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce ya kai wa Buhari ziyara ne domin ya gode masa.

“Na zo ne na gode wa Shugaba Buhari saboda ziyarar da ya kai mani a Landan lokacin da nake jinyar ƙafa. Ya nuna mani ƙauna. Shugaba ne na musamman,” in ji shi.

A watan Agusta ne Buhari ya ziyarci Tinubu bayan an yi masa tiyata a ƙafarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *