fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Tonon Silili: An gano yanda wasu jami’an tsaro ke cin Amanar kasa da karbar cin hanci a iyakokin Najeriya da kasashe Makwabta

Wani bincike da Jaridar Punchng ta yi, ya gano yanda wasu jamo’an tsaro akan iyakokin Najeriya ke karbar Na Goro su bari a fita da man fetur daga Najeriya zuwa kasashe Makwabta.

 

Binciken an yishine a iyakokin Najeriya dake jihohin Katsina, Sokoto, Borno, Kwara, Taraba, Adamawa da Ogun.

 

Lamarin yasa matsalar yawaitar kudin tallafin man fetur na kara yawa. A baya, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saka dokar hana kai man fetur a Kilometres 20 kusa da iyakokin Najeriya da kasashen waje.

 

Wannan kokarine na ganin an dakile fasakwaurin man da ake yi zuwa kasashen wajen.

 

Saidai za’a iya cewa kwalliya bata biya kudin sabuluba, saboda Karamin Ministan man fetur,  Timipre Sylva ya bayyana cewa, kudin tallafin man fetur na kara karuwa, yanzu ya kai Fala Biliyan 5.58.

 

Fasa kwaurin man fetur daga Najeriya zuwa wasu kasashen waje kasuwanci ne me kawo kudi sosai ga masilu yinshi. Misali, suna sayen man daga Najeriya akan Naira 163 zuwa 165 kan kowace Lita suna sayar dashi akan Nunki 3 na wannan kudi a jamhuriyar Nijar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *