fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Tonon Silili: Daga wajan DSS muke samun makamai, idan an biyamu kudin fansa, muna rabawa>>’Yan Bindiga

Peoplesgazette ta ruwaito cewa, Tsageran ‘yan Bindiga sun bayyanawa kafar watsa labarai ta kasar Jamus, Deutsche Welle cewa, a wajan jami’an DSS suke samun makaman da suke amfani dasu.

 

Hakanan sun kara da cewa, idan aka biyasu kudin fansa, a wani lokacin suna rabawa da jami’an.

 

Hakanan ‘yan Bindigar sun bayyana cewa akwai kuma hannun ‘yansanda a lamarin.  Peoplesgazette ta nemi jin ta bakin kakakin DSS kan ko suna sane da abinda ke faruwa? Amma bai bayar da amsa ba.

 

A baya dai, tsohon Shugaban Sojojin Najeriya,  Theophilus Danjuma ya zargi jami’an tsaro da baiwa ‘yan bindigar dake kai hare-hare a Arewa maso yamma makamai.

 

Saidai Gwamnatin tarayya ta karyata lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *