fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Tottenham ta lallasa Man City da 2-0: Mourinho ya dauki hankula sosai

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Manchester City da ci 2-0 a wasan da suka buga yau na neman cin kofin Premier League na kasar Ingila. Bergwijn da Son ne suka ciwa Tottenham kwallayen nata bayan da Zinchenko na City ya samu jan kati.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

City ta samu bugun daga kai sai Gola amma ta barar da damar inda a nanne Sterling dake da katin gargadi yayi faduwar da gangan dan neman sake samun bugun daga kai sai me tsaron gida amma VAR ta hana, Mourinho da masoya kwallo da yawa sun yi koken cewa ya kamata a baiwa Sterling jan kati saboda abinda yayi amma alkalin wasan bai bashi ba.

Mourinho ya dauki hankula sosai inda ya burge mutane bayan da ya nuna farin ciki da barar da damar bugun daga kai sai gola da City ta yi sannan kuma daga baya ya tashi ya nuna bacin ransa wajan rashin baiwa Sterling jan Kati.

Arsenal da Burnley kuwa sun tashi 0-0 ne


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *