fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Tsageran IPOB sun kaiwa gidan Gwamnan Jihar hari

Yan bindiga sun kai hari gidan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Jaridar The Nation ta tattaro sun mamaye gidan Gwamnan a Omuma a karamar hukumar Oru ta gabas a safiyar ranar Asabar.
Rahotanni sun ce sun kashe wasu jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki kafin su kona gidan.
Hakanan motocin da ke ajiye a harabar kuma wani bangare na ginin wutar ta shafa.
Kwamishinan yada labarai da dabaru, Declan Emelumba, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa: “Gaskiya ne amma bayanin har yanzu bai bayyana ba. Ba gaskiya bane cewa jami’an tsaro da yawa sun rasa rayukansu ba. Kimanin jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki a gidan gwamnan sun mutu. Jami’an NSCDC na daga cikin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu yayin harin. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *