fbpx
Monday, September 27
Shadow

Tsageran IPOB sun sake saka wata sabuwar ranar zaman gida dirshan

Tsageran kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra sun sake saka wata sabuwar ranar zaman gida dirshan.

 

IPOB ta sanar da cewa, nan da 14 ga watan Satumba zata yi zaman gidan dole.

 

Kungiyar ta sanar da hakane ta bakin daya daga cikin Shuwagabannin ta, Mazi Chika Edoziem, kamar yanda PMnews ta ruwaito.

 

Tace kada wanda ya fito kasuwanci a waccan rana dan zata yi jimamin kisan da aka yiwa mutanen ta shekaru 3 da suka gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *