fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Tsagerun kungiyar ESN sun kashe sojoji biyu a Enugu

Tsagerun kungiyar ESN sun kashe sojoji biyu na sojojin Najeriya a jihar Enugu.

An kashe sojojin ne a ranar Talata a garin Adani na karamar hukumar Uzo-Uwani da ke jihar yayin da suke kokarin dakile harin bindiga na kungiyar ESN, Daraktan, Hulda da Jama’a na Sojojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

Wani sashi na bayanan ya karanta: “Abin takaici, yayin yakin wuta da ya afku, sojoji biyu sun biya mafi girman farashin.

“A yanzu haka sojojin suna kan bin sahun masu aikata laifi. ”

Nwachukwu ya bukaci jama’a da su samar da bayanai masu amfani kan ‘yan bindigan da suka gudu ga rundunar.

“Muna tabbatar wa da sauran al’umma kudurinmu na samar da isasshen tsaro a yankin baki daya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa “Muna kuma yin kira ga jama’a da su ba da himma ga jami’an tsaro ta hanyar kasancewa masu bin doka da oda da kuma samar da bayanai masu amfani kan ‘yan bindigar da suka tsere.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *