fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Tsare ni kwanaki 30 da EFCC ta yi, tauye min ‘yanci ne>>Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani, ya bayyana cewa tsare shi tsawon kwanaki 30 da Hukumar EFCC ta yi, tauye masa ‘yanci ne karara aka yi.

Bayan an sake shi a ranar Alhamis, Sani ya fitar da sanarwar manema labarai a ranar Asabar cewa an danne masa hakki saboda kage da sharri da gadar-zaren da aka nemi a kulla masa.
“EFCC sun yi kokarin yin amfani da na’urar da ake jona wa mutum domin a gane karya ko gaskiyar sa. An kulle min asusun ajiya na banki. An binciki gida na, an binciki ofis di na, don kawai a samu laifin da za a rayata min a wuya, daga zargin wai na karbi dala 24,000.00 ko 25,000.00 daga hannun wani.”
Sani ya yi ikirarin cewa sharri ne aka nemi kulla masa, kage ne, yarfe ne, tuggu ne, gadar-zare ce kuma makarkashiya ce, kuma kutunguilar siyasa ce aka nemi yi masa.
An tsare shi a ranar 2 Ga Janairu, an kuma bada belin sa a kan kudi milyan 10 a ranar Alhamis aka sake shi.
Sani ya ci gaba da cewa mutuncin Najeriya zai ci gaba da zubewa a idon duniya, matsawar hukuma kamar EFCC za ta rika amfani da irin salon tsarin mulkin Hilter wajen cin zarfi da tauye hakkin kananan na kasa, a gefe guda kuma ana kyale gurzagullan barayi su na cin karen su babu babbaka yadda suka ga dama.
Da EFCC ta Tsare Ka, Gara Masu Garkuwa Su Tsare Ka -Shehu Sani a BBC Hausa
Da ya ke ci gaba da ragargazar EFCC bayan ya fito daga tsarewar kwanaki 30 da ta yi masa, tsohon sanatan bayyana wa BBC Hausa cewa da jami’an EFCC su tsare ka, har gara masu garkuwa su tsare ka.
Ya ce domin su masu garkuwa idan suka nemi kudi suka samu, to sakin ka za su yi.
Haka ya bayyana a cikin wani bidiyo da BBC ta watsa a shafukan ta na soshiyal midiya.
Idan ba a manta ba, bayan da EFCC ta kama Shehu Sani ta tsare shi, bayan ya shafe kwanaki, ta sake garzaya Babbar Kotun Abuja, ta nemi Mai Shari’a ya ba ta iznin ci gaba da tsare shi tsawon wasu kwani har 14, domin ta ci gaba da binciken sa.
An dai zarge shi da karbar dala 25,000 daga Sani Dauda, wani sanannen dan kasuwa a Kaduna, bisa cewa zai kai wa Cif Jojin Najeriya, Muhammad Tanko da kuma Shugaban EFCC Magu, domin Dauda ya samu sa’idar wata mataala da ke tartare da shi.
Sai dai kuma har bayan sakin da aka yi wa Shehu Sani, babu wani labarin cewa an kama Sani Dauda, wanda aka di sani da ASD Motors, domin dokar bada cin hanci har mai bayarwa ta shafa, ba mai karba kadai ba.
PThausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *