fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Tsohon kakakin majalisa ya harbe kansa domin gujewa amsa tambayoyi

Wani tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Malawi, Clement Chiwaya ya bindige kansa har lahira a farfajiyar majalisa a yayin halartar wani zaman sauraren bahasi kan wata tuhuma da ake masa.

Clement Chiwaya, mai shekaru 50 ya harbe kansa da harsashi ne a cikin zauren majalisar, inda ya halarci zaman wani kwamiti da ya bukaci ya yi bayani a game da motar da aka ba shi a shekarar 2019, a lokacin da yake kan mukaminsa na kakaki.

Kakakin ‘yan sandan kasar, James Kadadzera ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma kuma bai bada karin bayani ba, bisa dalilin cewa sai ya karbi cikakken rahoto daga masu bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *