fbpx
Friday, May 14
Shadow

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya kai ziyarar aikin kwana daya a Jihar Sakkwato

Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar aikin kwana daya a Sakkwato

Olusegun Obasanjo ya ziyarci fadar mai alfarma Sarkin Musulmi inda ya yi wa mai martaba mubaya’a.

A fadar, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula da kuma bambancin ra’ayoyi marasa kyau tsakanin ‘yan Najeriya.

Ya ce takaddama tsakanin mabiya addinai daban-daban a kasar na yin barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasar.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya kuma yi kira ga Olusegun Obasanjo da ya yi amfani da matsayinsa da iliminsa na addini wajen hada kan mabiya Addinin Musulunci da Kiristanci wuri guda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *