fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Tun bayan Mutuwar Abubakar Shakau, Sojojin Najeriya sun gano lagon Boko Haram sai kashesu suke, amma Boko Haram din ta fito da wata dabarar kaucewa kisan Sojojin

Tun bayan Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau,  Lamarin Kungiyar da ta ISWAP data balle daga cikinta suka yi kasa.

 

A ‘yan kwanakinnan, Sojojin Najeriya sun dage da aki musu hari, sai kashe Shuwagabannin kungiyar suke, ciki hadda wanda ya jagoranci gumurzun da ya kashe Abubakar Shekau.  Ko da a jiya, an ji yanda Sojojin Najeriya suka kashe wani hatsabibin kwamandan ISWAP da akewa lakabi da Janar me Ido daya.

 

A yanzu ISWAP karkashin Jagorancin shugabanta, Mus’ab Albarnawi na neman bin sahun uwar kungiyarsu ta Boko Haram wajan boyewa a cikin duhuwar daji, maimakon a sarari da suke gudanar da ayyukansu.

 

Sojojin Najeriya na da masu basu bayanan Sirri wanda da zarar ISWAP sun taru suna son yin wani gangami, sai Sojojin su kai musu hari su karkashesu.

 

Defence Nigeria ya ruwaito cewa, Yanzu ISWAP ya shirya Kwaikwayar Boko Haram wajan Boyewa a cikin Duhuwa da tsaunuka inda Keea Sojoji wahalar Shiga. Sanna kuma Suna son fafada wa zuwa shiga Jihar Kaduna saboda Dajin dake can.

 

They know the jungle like Nigerian troops do not. ISWAP is now relying on Boko Haram’s decades long experience to move their base of operations from the open grasslands of Lake Chad to thick jungles of Borno and Kaduna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *