fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Tunda kake ka taba ganin taron jama’a da yawa haka? Ministan Harkokin waje na Iran ya gayawa Shugaban Amurka kan jana’izar Sojanta

Ministan harkokin kasashen waje na kasar Iran, Javad Zarif ya gargadi shugaban kasar Amurka, Donald Trump da cewa kada ya saurari masu zugashi akan yankin gabas ta tsakiya da kuma tunanin cewa zai iya karya kadarin kasar Iran.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ya bayyana hakane a shafinshi na Twitter inda ya ja hankalin Shugaban Amurkar da cewa shin ya taba ganin tarin jama’a da yawa haka a rayuwarshi?

Ya kara da cewa, karshen zaman Dakarun kasar na Amurka a yankin gabas ta tsakiya ya zo.

Dubbunnan Mutanene suka taru a titunan Tehran dan nuna Alhinin kisan da kasar Amurka ta wa kwamandan sojin kasar, Qassem Soleimani. Rahotan sun bayyana cewa wannan ne taro na farko da kasar ta yi na hadun kai a kan mutum 1.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *