fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Uwa da danta sun gurfana a Kotu bisa laifin lakadawa dansanda dukan kawo wuka

Wata mata, Aminat Salami me shekaru 45 da kuma danta, Abiodun Salami me shekaru 22 sun gurfana a gaban kotun Magistre dake Ikeja, Jihar Legas saboda Lakadawa Dansanda dukan kawo wuka.

 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito cewa sun aikata laifinne ranar 6 ga watan Janairu yayin da aka je kama mijin Matar, Nurudeen Salami wanda ya tsayawa wani da aka bada belinsa amma ya kasa kawoshi wajan shari’a.

Dansanda me gabatar da kara yace dalilin hakane minin da aka je kamawa ya tsere. Mai Shari’a,  O.A Odubayo ta bayar da belin wanda ake zargi kan Naira 100,000 da kuma wanda zai tsaya musu.

 

Ta kuma dage sauraren shari’ar har sai zuwa 3 ga watan Fabfairu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *