fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Uwa ta cakawa diyarta kwalba ta mutu saboda kwana a waje

Wata Mahaifiya ta cakawa diyarta Kwalba ta mutu saboda ta kwana a waje.

 

‘Yansanda a jihar Osun sun kama Kafayat Lawal saboda kashe diyarta, Ayomide Adekoya.

 

Yarinyar me shekaru 17 da ‘yar uwarta sun kwana a waje wanda baiwa uwar dadi ba, wajan rikicin lamarin, matar ta kuma cakawa dayar diyarta kwalba a hannu wanda tana asibiti tana karbar magani.

 

Kakakin ‘yansandan Jihar, Abimbola Oyeyemi ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.

 

Yace tun da sallah Mahaifiyar ta kai kara wajan ‘yansanda cewa ‘ya’yanta 2 bata san inda suke ba sun bace. Saidai daga baya sun dawo, ta so ta dakesu amma aka bata baki.

 

Matar da tace ta rabu da mijinta, shekaru 9 da suka gabata, ranta ya baci ta sake kama ‘ya’yan nata da duka bayan da suka sake kwana a waje, a nan ne ta jiwa daya rauni a kirji daya a hannu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *