fbpx
Monday, November 29
Shadow

Wajibine gwajin Lafiya kamin Aure>> Sheikh Daurawa

Bayan an binciki halin mutum da addinin sa da sana’arsa. Wajibi ne kuma lallai akwai buƙatar anyi bincike sosai domin a tabbatar da lafiyar ma’aurata.

Domin rashin yin bincike ya jawo matsala da yawa na lalacewar aure da kamuwa da cututtuka masu wuyar sha’ani. Kamar gwajin cutar ƙanjamau, gwajin sikla, awon ciki, domin a tabbatar babu ciki tare da ita.
Sai kuma gwajin ciwon sanyi, gwajin duk wata cuta da ake tsammanin ɗauka, domin kare lafiyar ma’aurata, da zuriya daga ciwon da za a iya tsarewa, abinda ba a sani ba kuma sai ayi addu’a a barwa Allah.
Wasu jihohi sun mayar da shi doka, ya kamata duk wanda zai yi aure ya je a yi gwaji.
Allah ya tsare mana lafiya


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *