fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Wanda har yanzu suke amfani da Twitter zasu dandana kudarsu>>Hadimin Abubakar Malami

Hadimin Abubakar Malami, Dr. Umar Gwandu ya bayyana cewa, wanda har yanzu ke amfani da manhajar Twitter a Najeriya zasu dandana kudarsu nan gaba kadan.

 

Babban Lauyan gwamnati,  Abubakar Malami ya bayyana cewa za’a hukunta wanda har yanzu suke amfani da shafin na Twitter a wata sanarwa da ya fitar.

 

Premium times ta tuntubi Umar Gwandu dan jin wace doka ce za’a yi amfani da ita wajan  hukunta ‘yan Najeriya amma yace idan aka kaisu kotu zasu ji dokar da za’a yi amfani da ita.

 

Da aka matsa masa, sai yace dokar Gwamnatin Tarayya ce.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *