fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Wani dalibi ya mutu yayin da ginin dakunan kwanan dalibai ya rufta a Jihar Adamawa

Wani dalibi mai suna Harka Yinasimna ya mutu lokacin da wani ginin kwanan dalibai a makarantar sakandaren Gwamnati, Numan a jihar Adamawa ya fado masa a ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni.

A cewar rahotanni, ginin ya rushe lokacin da aka fara ruwan sama. Marigayin ya kasance yana barci lokacin da ginin ya fado masa.

Wani dalibin makarantar ya bayyana cewa wasu gine ginen makarantar da suka hada dakin kwanan dalibai, azuzuwan karatu da sauransu, suna bukar gyare-gyare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *