fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Wani dan jaridar Najeriya ya mai da dala $3,000 da ya bata ga mai shi

Abdulkadir Shehu, dan jarida mai aiki a gidan rediyon Progress FM a Gombe ya mayar da dala $ 3,000 da ya samu a kan hanyar ga mai shi.
Shehu ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa yana da kasa da N2,000 a aljihunsa a lokacin da ya tsinci kudin.
Dan jaridar ya ce lokacin da ya gano kudin, sai aka kira shi daga Kano cewa dan nasa ba shi da lafiya kuma yana bukatar a yi masa gwajin cutar koda da hanta.
“Ba za su iya ci gaba ba saboda babu kudi. Har yanzu yana cikin kulawar likita, ”in ji shi.
Shehu ya jaddada cewa talauci bai kamata ya zama hujja ta rashin gaskiya ba, ya kara da cewa Allah zai yi masa hukunci idan ya kashe kudin.
“A Musulunci, Manzon Allah ya gaya mana cewa duk wanda ya samu wani abu da ya bata a cikin gari, to ya nemi mai shi tsawon shekara.’ ’
Shehu ya ce yana zuwa ofishin a ranar Laraba da ta gabata da misalin karfe 7 na safe, sai ya ga ambulan a kan hanya.
Dan jaridar ya sanar da abokan aikinsa amma bai bayyana adadin da kudin ba.
Daga baya ya sanar a rediyo cewa duk wanda ya yi yarda kudi a yankin to ya kira lambar wayarshi.
“Mai kudin ya kira, ya yi kuka mai zafi, ya bayyana wurin da ya rasa kudin, abin da kudin ya kunsa, jimillar kudin, da sauran bayanai”
Shehu ya kara da cewa bayan sanarwar, mutane kusan 50 sun kira sun nemi mallakar kudin amma babu wanda ya ba da ainihin adadin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *