fbpx
Friday, May 14
Shadow

Wani daya daga cikin yan bindingar da suka sace yaran makarantar Kankara ya koma daji makonni bayan da yace ya tuba

Auwal Daudawa, shugaban ‘yan bindinga a jihar Zamfara, wanda aka ce shi ne ya shirya satar dalibai sama da 300 a makwabtan jihar, Katsina a ranar 12 ga Disamba, 2020, ya koma daji makonni bayan ya sanar da tubarsa kuma ya mika makaman sa.

Makonni bayan sakin yaran, Daudawa da sauran mukarrabansa su biyar sun mika bindigogin AK 47 guda 20, alburusai da kuma makamai masu linzami (RPG) ga gwamnatin jihar Zamfara a ranar Litinin, 8 ga watan Fabrairu.

Sai dai, wani rahoto da DailyTrust ta wallafa ya ce Daudawa ya koma daji don daukar makamai.

A cewar rahoton, Daudawa ya bayar da rahoton cewa ya tattara iyalensa da sauran hadimansa zuwa dajin Jaja da ke karamar Hukumar Zurmi a ranar Litinin, 26 ga Afrilu.

Rahoton yace, Daudawa ya bayyana takaicin rashin samun sahihin aiki bayan ya ajiye makaman sa.

Shi da membobin kungiyar sa da suka tuba sun kasance a cikin gidan gwamnati a makonni kafin a yi masa gida a Damba, a gefen Gusau, don zama tare da iyalinsa.

Masu sharhi kan al’amuran tsaro a jihar sun ce abin da Daudawa ya yi babban koma baya ne ga yarjejeniyar zaman lafiya da kuma yin afuwa ga ‘yan bindinga da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ke tallatawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *