fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Wani direban tasi da karen mota, sunyiwa wata mata mai dauke da cutar kanjamau fyade

Wata fasinja ‘yar shekara 25 da ake zargin wani direban tasi da kwandastan sunyi wa fyade a ranar Litinin, ta ce ta ji tsoron bayyana masu cewa tana dauke da kwayar cutar ta HIV domin su mata barazana da bindiga.

Matar wadda aka jefar a gefen hanya‚ ta fadawa jami’an tsaro na Reaction Unit SA (Rusa) a ranar Litinin, tana son ta sanar da wadanda suka yi mata fyade cewa tana dauke da cutar kanjamau amma tana tsoron su harbe ta.

Mai magana da yawun Rusa, Prem Balram ya ce wani direban da ke wucewa ne ya kira su, inda nan take suka isa wajen.

Ya kara da cewa tuni amfara bincike a kan lamarin kafin a gabatar da lamarin gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *