fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Wani Kwamishinan a Jihar Borno ya rasa ‘yan uwansa uku a hadarin mota

Kwamishinan Gyare-gyare da tsara matsugunni na Borno (MRRR) Engr Mustapha Gubio, ya rasa yan uwa uku a wani mummunan hatsarin mota.

An tattaro cewa hatsarin motar ya afku ne akan titin Gubio/Magumeri a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.

Kwamishina

Wasu mutane biyu da suka hada da mace da direba suma sun halaka a hadarin mota.

Za a yi jana’izarsu da karfe 10 na safe a ranar Talata, 14 ga Satumba, a gidan Kwamishinan, a kan hanyar Damboa daura da Mafoni Liberty Primary and secondary school, Maiduguri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *