fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Wani makiyin Musulunci da musulmai ya yi amfani da babbar mota ya kashe mutane 4 ‘yan gida daya

Wani mutum da yake kin jinin Musulunci da musulmai ya buge wasu mutane 5 ‘yan gida daya kuma 4 daga ciki sun mutu.

 

Yaro dan Shekaru 9 ne kawai ya tsira a cikinsu.  Lamarin ya farune a Ontario dake birnin Landan a kasar Canada inda iyalan suka fita yawon Shakatawa ranar Lahadi.

 

Wands aka kashe sune, Madiha Salman, Salman Afzal, Yumna Salman. Wanda ya kashesu, Nathaniel Veltman dan kimanin Shekaru 20 ya bayyana cewa ya kashesu ne kawai dan ya tsani Musulunci.

 

Za’a cajeshi da Kisan kai da kuma aikin ta’addanci, wanda ya kashe din ‘yan kasar Pakistan ne da suka shafe shekaru 14 a kasar Canada.

 

Firaiministan kasar, Justin Trudeau ya bayyana kaduwa kan lamarin

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *