fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Wani masoyin Gwamnan Gombe ya fado daga Mota ya mutu yayin da yake tare da tawar gwamnan

Matashi dan shekaru 30, Ahmad Sagir wanda aka fi sani da Khalifah ya bayyana cewa ya fado ya mutu yayin da yake tare da tawagar gwamnan jihar Gombe,  Muhammad Inuwa.

 

Gwamnan na kan hanya ne yayin da lamarin ya faru inda ya bayar da umarnin daukar matashin a kaishi asibiti.

 

Likitoci sun tabbatar da mutuwar matashin. Inda hakan yasa gwamnan ya dskatar da tafiye-tafiyensa na ranar.

 

Sakataren yada labaran Gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *