fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Wani matashi ya dabawa abokinsa wuka har lahira saboda wayar tarho a Jihar Adamawa

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Adamawa ta cafke wani matashi dan shekaru 18 da ake zargi da daba wa abokinsa mai shekaru 21 wuka har lahira a yayin wani fada da suka kan wayar Infinix a karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar.

Wanda ake zargin, Abdulkarim Adamu mai shekaru 18, dan asalin jihar Gombe, an kama shi ne a ranar Talata, 14 ga Afrilu, bayan ya kashe abokinsa mai suna Ayuba Hassan, wanda ya zarge shi da satar wayarsa ta N55,000.

Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Yola, Abdulkarim ya ce marigayin ya kira shi tare da abokansu biyu inda duk suka hadu kuma suka hada baki suka je suka saci jarkoki dauke da mai a wani gidan mai da ke garin.

A cewar wanda ake zargin, sun koma gida ne domin kwanciya bayan basu yi nasarar satar jarkokin man fetur din ba, da daddare ya farka amma ko sama ko kasa bai ga wayarsa ba.

Abokansa biyu suka ce masa Ayuba ne kawai ya ziyarci gidan yayin da yake barci, a lokacin da ya tunkari Ayuba washegari, ya musanta daukar waya.

An yi artabu mai zafi sannan mutanen biyu, tare da rakiyar abokansu biyu, suka amince da zuwa bakin kogi domin cigaba da fadan.

Abdulkarim ya yi ikirarin cewa a kan hanyarsu ta zuwa bakin kogin, Ayuba ya jefe shi da dutse, wanda hakan ya sa ya zaro wuka ya daba masa sau biyu a hannu da kirji.

Wanda ake zargin, ya gudu daga wurin, ya bar abokinsa a cikin jini, daga baya kungiyar yan banga sun damke shi kuma suka mika shi ga yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Suleima Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zaran an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *