fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 a Jigawa – Hukumar Yan Sanda

Akalla mutane 18 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku ranar Laraba a kan hanyar Birninkudu zuwa Kano a karamar hukumar Birninkudu da ke Jigawa.

ASP Lawan Shisu, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na jihar ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shisu ya fadawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safe, kusa da gonar Alu.

A cewarsa, motocin biyu da hatsarin ya rutsa da su sun yi karo ne wanda ya haifar da gobara.

Ya ce, fasinjoji 12 sun kone kurmus ba tare da an san su ba yayin da shida daga cikinsu suka mutu nan take.

PPRO ya kara da cewa daya daga cikin direbobin motocin ne kawai ya tsira daga hatsarin, yana mai cewa yana karbar magani a yanzu haka a babban asibitin tarayya (FMC), Birninkudu.

Ya kuma ce an ijiye gawar wadanda suka mutu a dakin ijiye gawar na FMC.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *