fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Wani mutum ya boye gawar mahaifiyarsa tsawon shekara daya yana karbar fanshonta

Wani mutum ya boye gawar mahaifiyarsa a wani daki da ke kasan gidansa fiye da shekara daya yana karbar fanshonta, a cewae ‘yan sandan kasar Austria.

Ana tsammanin matar mai shekara 89, ta rasu ne sakamakon cutar mantuwa da ta yi fama da ita a watan Ynin bara.

An ce dan nata mai shekara 66 ya sanya gawar tata ne a rumbun da yake ajiye giya ya jibga kankara a kan gawar don hana ta wari.

‘Yan sanda sun yi amannar cewa ya karbi kusan fan miliyan 42,000 ba bisa ka’ida ba a cikin kudin fanshon nata.

An gano lamarin zambar ne bayan da wani mai kai sakon takardu ya ce an hana shi ganin matar a lokacin da ya bukaci hakan, a cewar sanarwar ‘yan sanda.

Hakan ne ya jawo aka fara bincike ya kuma sa aka gano abin da mutumin ya aikata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *