fbpx
Friday, May 14
Shadow

Wani mutum ya kone kurmus a wani hatsarin da ya rutsa da tireloli hudu da tankar mai a jihar Kwara

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe a ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, a babbar hanyar Bode Saadu-Jebba, karamar hukumar Moro ta jihar Kwara.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Hasan Adekunle ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon wuce gona da iri da direbobin suka yi, wanda hakan ya haifar da karo da juna.

Wannan hatsarin ya haifar da barkewar gobara tare da kona kayayyakin a cikin tireloli.

An kuma bayyana cewa wani mutum ya kone kurmus wanda ba za a iya gane shi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *