fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Wani mutum ya mutu sandiyyar nitsewa a rafi a jihar Kano

Wani Hamisu Ahmed, a ranar Asabar ya nitse a cikin wani rafi a Samegu bayan Sahad, jihar Kano.
NAN ta ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wanda lamarin ya rutsa da shi makanike ne dan shekara 20 wanda ya je wanka bayan ya gyara mota.
Abdullahi ya ce da misalin karfe 07:31 na safe, sai wani Muhammad Abdulmalik ya kira shi.
“Da samun labarin, nan da nan muka tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da misalin karfe 07:43 na safe,” in ji shi.
Abdullahi ya kara da cewa an fito da Hamisu daga cikin ruwan kuma an mika gawar ga mahaifinsa, Alhaji Yahaya Usman na Unguwar Dorayi Chiranci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *