fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Wani mutum ya rasa yaransa 3 sakamakon rushewar gini a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a ranar Litinin ta tabbatar da mutuwar wasu yara uku a sanadiyyar rushewar gini a karamar hukumar Ringim ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da mutuwar yaran a cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Litinin.

Shiisu ya ce ginin ya rufta ranar Alhamis a kauyen Yakasawa Kwari, Ringim, kuma mahaifin margayan, Malam Garba Lawan ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Ya ce da taimakon ‘yan sanda da wasu mazauna yankin, an cire margyan (Naima Garba, Umar Garba da Sale Garba) daga cikin tarkacen ginin inda aka garzaya da su zuwa Babban Asibitin Ringim, domin kula da lafiyarsu.

Kakakin ya ce daga baya likita ya tabbatar da mutuwar matasan a babban asibitin.

A cewarsa, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Aliyu Sale, ya yi kira ga mutanen jihar da su tabbatar da cewa gine -ginensu suna cikin yanayi mai kyau, musamman lokacin damina, don gujewa rushewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *