fbpx
Monday, May 10
Shadow

Wani mutum ya rataye kansa a gidan surukinsa bayan ya gano matar sa tana cin amanarsa

Wani matashi mai shekaru 30 ya rataye kansa bayan ya gano matar sa tana cin amanarsa.

Rahotannin sun nuna cewa Peter Mlauzi ya rataye kansa ne a gidan surukinsa bayan ya gano cewa matarsa ​​Blessing Manokore tana tarayya da wani namiji a waje.

Cif Gwesela ya tabbatar da cewa Mlauzi ya rataye kansa ne bayan da ya gano cewa matarsa na saduwa da wani mutum daga ƙauyen.

Cif Gwesela, yace wannan mummunan lamarin ya matukar tayar wa da mutanen yankin hankali.

Ya kuma bayyana marigayin a matsayin mutum mai kwazo sosai, wanda ke aikin hakar zinari domin kula da iyalansa da kuma surukansa.

Shugaban kauyen ya kuma bayyana cewa har yanzu bai sadu da Manokores ba don a gudanar da bikin mutuwarsa ba, saboda suna fargabar cewa lamarin na iya kawo mummunan rikicin a kauyen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *