fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Wani Sanata Ya Ba da Gudummawar Naira Miliyan 20 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kasuwar Katsina

Ahmad Babba Kaita, sanata mai wakiltar gundumar Katsina ta Tsakiya, ya jajantawa wadanda gobarar ta shafa inda ta lakume wasu sassan babbar kasuwar birnin.
Ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 don magance matsalolin ‘yan kasuwar da abin ya shafa. Ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya kai ziyarar tausayawa ga ‘yan kasuwar a ranar Asabar.
A nasa martanin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ya gode wa sanatan kan wannan karamci, da kuma duk sauran masu tausayawar da ke zuwa rukuni-rukuni da kuma daidaiku don sanin su.
A wani labarin makamancin wannan, mai martaba Sarkin Daura, Dr Umar Farouk Umar, shi ma ya kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Katsina kan abin da ya faru. Ya bukaci wadanda abin ya shafa su dauki abin da ya same su a matsayin wata jarabawa daga Allah kuma su yarda da shi da kyakkyawar niyya don samun cikakken sakamakon.
Ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa, sannan ya gode wa Gwamna Aminu Bello Masari kan jajircewar sa wajen sake gina kasuwar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *