fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Wani shirgegen Tauraron dan Adam mallakin kasar China ya kubuce mata ya nufo Duniya gadan-gadan, kuma ba’a san a wace kasa zai sauka ba

Wani shirgenen Tauraron dan Adam me nauyin Tan 21 mallakin kasar China ya subuce mata ya nufo Duniya gadan-gadan.

 

Ranar Asabar me zuwa ake tsammanin Tayraron dan Adam sin zai iso Duniya amma babu takamaiman bayani kan inda zai fado. Rahoton yace sai awanni kadan kamin isowarshi Duniya sannan za’a san inda zai fado.

 

Amma masana daga kasar Amurka sun yi amannar cewa zai fada ne inda babu Mutane, kamar yanda Mailonline ta ruwaito.

 

Kakakin tsaro na kasar yace zasu rika bayar da bayanai akai-akai kan zuwan tauraron dan Adam din a https://www.space-track.org/auth/login dan asan inda zai fadi.

 

Taurarin dan Adam da dama sun aiko da sakon rikitowar tauraron dan Adam din na kasar China me tsawon kafa 100 da fadin kafa 16.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *