fbpx
Friday, April 23
Shadow

Wani uba yayiwa dansa duka har lahira bisa zarginsa da sata a shagonsa

 

 

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano a ranar Laraba ta ce ta cafke wani uba mai suna Awaisu Auwalu, dan shekaru 40, wanda ya lakadawa dan sa mai shekaru 19 (Auwalu Awaisu) dukan tsiya har lahira saboda zargin sata.

Yan sanda sun ce Awaisu ya yi amfani da sanda ya yi wa dan nasa duka, wanda ya mutu kwanaki kadan bayan an garzaya da shi asibiti.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, DSP Abdullahi Haruna, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce mahaifin ya yi zargin dan nasa da yi masa sata a shagonsa.

A yayin bincike, mahaifin ya furta cewa ya yi amfani da sanda wajen dukan dansa.

Ya kuma bayyana cewa marigayin ya yi masa sata mai yawa a shagonsa na sayar kayan masarufi.

Saidai a halin yanzu Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ba da umarnin a tura karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar, don gudanar da bincike cikin hikima.

DSP Haruna ya kuma ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *