fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Wannan yafi abinda Boko Haram take Muni, kuma ba zamu Lamunta ba>>Kungiyoyin Arewa suka nuna bacin ransu kan yankan Ragon da IPOB tawa Fulani 19

Kungiyoyin Arewa dama masu Amfani da shafukan sada zumunta da suka fito daga yankin sun nuna bacin ransu kan yankan Ragon da akawa Fulani 19 ‘yan gida daya a jihar Anambra.

 

Kungiyoyin Sun yi takaicin cewa yawanci kafafen watsa labarai da idan a Arewa aka yi abu sukan alakantashi da Wata Kabila ko addini, amma sun kawar da kai kan wannan mummunan lamari.

 

Tace kuma ga wanda suka kawo Rahoton ma sun rika fadar cewa, ‘yan Bindigar ba’a sa ko suwanene ba amma a zahirin gaskiya ‘yan IPOB ne.

 

Kungiyoyin sun kuma bayyana cewa shiru daga shuwagabannin Inyamurai na cikin gida da kasashen waje ya nuna cewa, duka suna goyon bayan kungiyar IPOB.

 

Kungiyoyin Dattawan Arewa na NEF ta bakin kakakinsu, Hakeem Baba Ahmad da kuma CNG ta bakin kakakinta, Abdulaziz Sulaiman ne suka nuna bavin ransu.

 

Kungiyar CNG ta bayyana cewa, wannan abin da aka yi yafi abinda ‘yan Bindiga da Boko Haram ke yi Muni.

 

Da Daily Trust ta tuntubi hukumar ‘yansanda ta jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin amma tacr mutane 9 ne kawai aka kashe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *