fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Wasu da aka kama bisa zargin ‘yan Bindiga ne sun bayyana cewa ‘yansanda na neman su biya Miliyan 35 kamin a sakesu

 

Wasu ‘yan uwan juna, Bawa Adamu da Abdullahi Adamu da aka kama bisa zargin ‘yan Bindiga ne a jihar Nasarawa sun bayyana cewa, suna zargin hukumar ‘yansandan jihar da neman su biya Miliyan 35 kamin a sakesu.

 

Sun bayyana hakane a cikin wata wasika da suka aikewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Shugaban ‘yansandan Najeriya,  IGP Usman Baba.

 

Sun bayyana cewa su 17 aka kama inda aka saki 12, amma su da wasu 3 da suka rage an ce sai sun biya Miliyan 35 kamin a sakesu. Sun bayyana cewa basu aikata laifin komai ba.

 

Saidai Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Bola Longe ya musanta wannan lamari inda yace, tun bayan da aka kama mutanen suke samun matsin lamba kan a sakesu.

 

Yace babu wanda zai bata musu suna kan aikin da suke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *