fbpx
Friday, May 14
Shadow

Wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kashe wasu manoma 9 a Jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kashe sama da mutane tara tare da jikkata da dama yayin wani hari da suka kai Ajimaka, wani matsugunin Tiv da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.

An bayyana cewa yan bindigan sun afkawa mutanen ne dauke da muggan makamai da misalin karfe 2:00 na safiyar Asabar, suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Ajimaka gari ne mai iyaka tsakanin Nasarawa da jihar Benue mallakar manoma Tiv.

Yawancin wadanda abin ya rutsa da su an ce sun yi barcin sosai lokacin da makiyayan suka kewaye kauyen, suka cinnawa gidaje wuta tare da bude wuta kan mazauna kauyen da ke gudu.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Doma, Hon Atukpa Osukunu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya ce ramuwar gayya ce.

Ya yi ikirarin cewa makiyayan, wadanda suke zauna a yankin, sun sami gawar daya daga cikinsu ya mutu a cikin daji kuma suna zargin cewa mutanen Tiv ne suka kashe shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *